Back to Languages

Hausa - Chapter 65 - At-Talaq

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah At-Talaq 65:1

Ya kai Annabi! Idan kun saki mata, sai ku sake su ga iddarsu,* kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidajensu, kuma kada su fita face idan suna zuwa da wata alfasha bayyananna. Kuma waɗancan iyakokin Allah ne. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to, lalle ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ɗammanin Allah zai fitar da wani al'amari a bayan haka

Verse 2 — Surah At-Talaq 65:2

Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani ko ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da masu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar domin Allah. Wancan ɗinku ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita

Verse 3 — Surah At-Talaq 65:3

Kuma Ya arzuta shi daga inda ba ya zato. Kuma wanda ya dogara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙiƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kome

Verse 4 — Surah At-Talaq 65:4

Kuma waɗanda suka yanke* ɗammani daga haila daga matanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu wata uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abuta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa

Verse 5 — Surah At-Talaq 65:5

Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa munanan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sakamako

Verse 6 — Surah At-Talaq 65:6

Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar* daga gwargwadon samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abuta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shayar da mama saboda ku, sai ku ba su tsadodinsu. Kuma ku yi shawara a tsakaninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nuna talauci to wata mace za ta shayar da mama saboda shi (mijin)

Verse 7 — Surah At-Talaq 65:7

Sai mawadaci ya ciyar daga wadatarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya kallafa wa wani rai face abin da Ya ba shi. Allah zai sanya sauƙi a bayan tsanani

Verse 8 — Surah At-Talaq 65:8

Kuma da yawa* daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisabi, hisabi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azaba abar ƙyama

Verse 9 — Surah At-Talaq 65:9

Sa'an nan ta ɗanɗana masifar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasara

Verse 10 — Surah At-Talaq 65:10

Allah Ya yi musu tattalin wata azaba mai tsanani. Saboda haka ku bi Allah da taƙawa, ya ma'abuta hankula, waɗanda suka yi imani! Haƙiƙa Allah Ya saukar da wata tunatarwa zuwa gare ku

Verse 11 — Surah At-Talaq 65:11

Manzo, yana karatun ayoyin Allah bayyananu a kanku domin Ya fitar da waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi imani da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidajen Aljanna ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu har abada. Haƙiƙa Allah Ya kyautata* masa arziki

Verse 12 — Surah At-Talaq 65:12

Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasa kwatankwacinsu, umuruin Sa yana ta sauka a tsakaninsu domin ku san lalle Allah Mai ikon yi ne akan dukan kome, kuma lalle Allah, haƙiƙa Ya kewaye ga dukan kome da sani