Kuma a sa'ilin da Annabi ya asirta wani labari zuwa ga sashen matansa, to, a lokacin da ta ba da labari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sashensa kuma ya kau da kai daga wani sashe. To, a lokacin da ya ba ta labari da shi, ta ce: "Wane ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartawa, Ya gaya mini
Idan ku biyu kuka tuba zuwa ga Allah, to, haƙiƙa zukatanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki juna a kansa to, lalle Allah Shi ne Mataimakinsa, da Jibrilu da salihan muminai. Kuma mala'iku a bayan wancan, mataimaka ne
Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu matan aure mafiya alheri daga gare ku, Musulmai muminai masu tawali'u, masu tuba, masu ibada, masu, azumi, zawarori da 'yammata
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kare wa kanku* (da iyalinku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala'iku masu kauri, masu ƙarfi. Ba su saɓa wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarnin su)
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku koma zuwa ga Allah komawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyagun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu a ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi *da wadanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, "Ya Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lalle Kai, a kan dukkan kome, Ya kai Mai ikon yi ne
Allah Ya buga wani misali domin waɗanda suka kafirta*: matar Nuhu da matar Luɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bayi biyu daga bayin Mu salihai, sai suka yaudare su, saboda haka ba su wadatar musu da kome daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, ku biyu, wuta tare da masu shiga
Kuma Allah Ya buga wani misali domin waɗanda suka yi imani; matar Fir'auna,* sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurin Ka a cikin Aljanna. Kuma Ka tsirar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsirar da ni daga mutanen nan azzalumai
Da Maryama* ɗiyar Imrana wadda ta tsare farjinta, sai Muka hura a cikinsa daga ruhinMu. Kuma ta gaskata game da ayoyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhali kuwa ta kasance daga masu tawali'u